Katsina: An Damƙe Wanda Ya Yi Sata Gidan Surukai

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta cafke Abdullahi Umar dan shekara talatin da daya, dan asalin garin Kari a karamar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna bisa zargin satar kayayyakin sanya wa a gidan su yarinyar shi da ya zo bakunta.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya yi baje-kolinsa a helkwatar rundunar da ke cikin garin Katsina.

A Lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, Abdullahi Umar ya ce mun hadu da ita a kafar sada zumunci ta Facebook, na ce mata zan zo Katsina ta ce in zo, na shirya na zo, ta tarbe ni hannun bibiyu, na kwana biyu a dakin yayanta, cikon na ukku da zan tafi na sace na’urar mai kwakwalwa ta laptop da hulunan sa ukku da kayan sawa. Na shiga gudan dakin na dauki takalman sawa kafa ukku, a cewarsa

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Labarai Makamanta