Katsina: An Cafke Barayin Da Suka Sace Miliyoyi A Gidan Gwamnati

Rahoton dake shigo mana daga birnin Katsina na bayyana cewar yanzu haka dai wasu jami’ai a ofishin gwamnan jihar na hannun ‘yan sanda bisa zargin satar wasu makudan kudade da ba a bayyana adadinsu ba a ofishin gwamna a daren Lahadi.

Majiyoyi sun ce kudin da aka sace sun kai N31m, duk da cewa babban daraktan Gwamna Aminu Masari kan sabbin kafafen yada labarai, Al-Amin Isah, ya ce bai san adadinsu ba.

An kuma bayyana cewa an yi satar ne a daren Lahadi a lokacin da ake tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya, a garin na Katsina.

Al- Amin Isah ya shaida wa manema labarai cewa: “‘Yan sanda sun kama wadanda ake zargin suna da hannu a satar. Tuni kuma aka fara bincike. Amma, ban san adadin da ake zargin sun sace ba.” Masu binciken sun ci gaba da bayyana cewa, an ga hoton wani mutum da ya saci kudin ta na’urar daukar hoto da aka sanya a ofishin mai kula da harkokin kudi da ke ofishin gwamnan.

Daya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa: “An ga barawon ne a na’urar CCTV a ofishin kula da harkokin kudi. Ya shiga ofishin ne ta taga. An kuma gan shi yana barin ofishin da wata katuwar jaka wacce ya zuba kudin a ciki.”

Kokarin jin karin bayani daga kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, SP Gambo Isah ya ci tura.

Labarai Makamanta

Leave a Reply