Katsina: Akwai Lauje Cikin Nadi A Kisan Da Aka Yi Wa Kwamishina – Masari

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Gwamnan jihar Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa kisan Kwamishanan Kimiyya da Fasahar jihar da akayi da lauje cikin nadi.

Masari yace duk da matsalar tsaro da annobar yan bindiga masu garkuwa da mutane, yadda aka kashe Dakta Rabe daban ne. Ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin tawagar gwamnatin tarayya da suka kawo ziyarar jaje.

Gwamnan yace ba’a dauki komai a gidan ba kuma ba’ayi garkuwa da kowa ba. Ko balla kofa ba’a yi ba, tabbas da akwai lauje cikin nadi.

“Ba da bindiga aka kasheshi ba, da wuka aka kashe shi, ba’a sace komai na shi ba. Kuma ba’a balla gidan ba.”

Gwamnan yace mutum biyu ke iya kashe Kwamishanan, wanda ke tare da mamacin ko kuma dan gidan. “Kamar yadda na fada, abinda mutum zai fahimta shine, duk wanda ya aikata wannan abin to mamacin ya bashi daman shiga dakin, ko kuma wanda ke da mukullan shiga dakinsa.” “Amma na san binciken jami’an tsaro zai bayyana abinda ya faru.”

An gudanar da Sallar Jana’izarsa karkashin jagorancin Limamin Masallacin Katsina GRA, Dr Aminu Abdullahi Yammawa. An bizne marigayin ne a makabartan Gidan Dawa bayan Sallar Jana’izar.

Wadanda suka halarci Jana’izar sun hada da Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari da tawagar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin mai bada shawara kan lamuran tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno.

Labarai Makamanta