Kashim Shettima Ne Shugaban ‘Yan Boko Haram – Naja’atu Mohammed

Kwamitin yaƙin neman zaben ɗan takarar kujerar shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 na jam’iyya PDP Alhaji Atiku Abubakar ya shiga jihar Kebbi a ranar Asabar, 28 ga watan Junairu, 2023.

Dan takarar shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar; abokin tafiyarsa, Ifeanyi Okowa; shugaban jam’iyyar, Iyorchia Ayu da sauran jiga-jigai sun dira Kebbi domin tallata Atiku.

“Mun tabbata PDP ta cinye Kebbi. Ni kuma a matsayina na dan takarar shugaban kasa, idan kuka zabeni zan tabbatar muku da abubuwa guda uku – rashin tsaro dake fama a Kebbi da sauran jihohi arewa maso yamma zamu magance.. da yardan Allah zamu dawo da zaman lafiya” Inji Atiku

Batun Dam din jihar Kebbi dake ba manoma ruwa har da Sokoto, muna tabbatar muku za mu yashe Dam din don dawo da ruwa – Na dauki alkawari zan bude boda. Gaba daya cikin yan takara babu wanda ya san harkar Boda kama na. Zamu bude boda domin kasuwanci.

“Mun sani, mun iya, mun yadda za mu yi.” “Ina jajanta muku game da kashe-kashe da akayi da kuma ambaliyar ruwa. Allah ya kiyaye.”

A jawabin da ta gabatar a yayin gangamin taron sananniyar ‘yar siyasar nan ta Jihar Kano Hajiya Naja’atu Mohammed ta bayyana cewa dan takaran mataimakin shugaban kasa na APC, Kashim Shettima, shine shugaban yan ta’addan Boko Haram.

Ta bayyana cewa Allah ya kiyaye shugaban ‘yan ta’adda ya zama mataimakin shugaban kasa a Najeriya. Ta ce dalilin da ya sa ta fadi hakan shine lokacin da Kabiru Sokoto, dan Boko Haram ya kai harin Bam cocin Katolika a jihar Neja, gidan Kashim Shettima ya boye.

Labarai Makamanta