Kashe Shekau: ISWAP Ba Ta Cancanci Tukwici Ba – Amurka

Ƙasar Amurka ta bayyana cewa ƙungiyar ISWAP ba zata samu ko sisi ba daga cikin dala miliyan $7m data sa kan duk wanda ya gano inda Abubakar Shekau yake.

Yayin da take martani kan rahoton mutuwan shugaban mayaƙan Boko Haram ɗin, Amurka tace ba zata baiwa ƙungiyar dake ƙarƙashin ISIS ba ko sisi.

Wannan na ƙunshe ne a wani rubutu da sashin shari’a na ƙasar Amurka yayi a shafinsa na Tuwita @RFJ_USA, rubutun ya bayyana cewa: “Rahoton da muka samu yau ya nuna cewa shugaban ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya kashe kansa a wata fafatawa da suka yi da mayaƙan ISWAP dake biyayya ga ISIS.”

“Baku cancanci tukuicin da muka sa ga wanda ya bada bayanan inda yake ba, haka shirin namu ya ƙunsa.”

Ya bayyana cewa a ranar 21 ga watan Yuni, 2012, sashin shari’a na ƙasar Amurka ya bayyana shugaban ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Sheƙau, a matsayin ɗaya daga cikin yan ta’addan duniya.

Bayan shekara daya da saka sunan Abubakar Shekau, sashin ya sanya tukuicin dala miliyan $7m ga duk wanda ya kawo bayanan inda maɓoyarsa take.

Labarai Makamanta

Leave a Reply