Kasashen Musulmi Sun La’anci Kisan Da Aka Yi Wa Matafiya A Sokoto

Rahoton dake shigo mana yanzu haka na bayyana cewar babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi (OIC), Hissein Taha, ya bayyana kakkausar suka kan harin ta’addanci da aka kai kan wata motar bas din fasinja a yankin ƙaramar Hukumar Sabon Birnin Gobir dake Jihar Sokoto.

Idan baku manta ba, a makwan jiya ne wasu ‘yan bindiga suka tare wata mota, suka banka mata wuta, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 42 nan take.

Harin ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 40 tare da jikkata wasu da dama. Babban sakataren ya bayyana harin a matsayin zalunci daga matsorata sannan ya bayyana jaje daga OIC ga gwamnati da al’ummar Najeriya a wannan mawuyacin lokaci.

Ya jajanta wa wadanda wannan bala’i ya rutsa da su, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

Labarai Makamanta