Kasar Arewa Ta Zamo Makarbarta – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmin Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar na 3 ya koka da cewa babu wata rana da ba za a kashe al’umma a Arewacin Nijeriya ba.

Sarkin Musulmin kuma ya shawarci ƴan Nijeriya da su haɗa kansu don kawo karshen ta’addanci a ƙasar.

A lokacin da yake tsokaci kan matsalar tsaro a Nijeriya a taron Majalisar Haɗin kan Addinai, NIREC, Sultan ya ce ba lokaci ba ne da mabiya addinai, musamman Musulmi da Kirista za su riƙa zargin juna da yi wa juna barazana ba.

Sarkin Musulmin ya nuna damuwa kan yadda kashe-kashe da sace-sacen jama’a ke ci gaba da afkuwa, amma kuma Musulmi da Kirista sun ɓige da nuna wa juna yatsa da yi wa juna barazana.

Labarai Makamanta