Kasafin Kudin 2022: Majalisa Ta Amince Da Tiriliyan 17

Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar bayan watanni biyu suna tattauna a kai, yan majalisar wakilai sun amince da daftarin kasafin kudin Shekarar 2022.

‘Yan majalisan sun yi wasu sauye-sauye cikin abinda Shugaba Buhari ya gabatar a kasafin Daga ciki akwai karawa wasu ma’aikatu kudi da kuma kiyasin farashin danyen man fetur.

Majalisar wakilan tarayya a ranar Talata, 21 ga Disamba 2021, ta amince da daftarin kasafin kudin 2022 da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabata mata a watan Oktoba.

Maimakon Naira Tiriliyan 16.39 da Buhari ya gabatar, yan majalisan sun kara sama da bilyan 700 a kai zuwa N17.126 trillion.

An ruwaito cewa majalisar ta kara N400bn wa ma’aikatu irinsu INEC, Majalisar dokoki da ma’aikatar tallafi da jin kai, dss. Majalisa kuma ta kara kiyasin farashin danyen mai daga $57/ganga zuwa $62/ganga.

‘Yan majalisan kuma sun ce hukumar EFCC da NFIU su rika amfani da kashi 10% na kudaden da suka kwato don karfafa yaki da rashawa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply