Karya Ne Babu Wanda Ya Gayyaceni Hukumar EFCC – Kwankwaso

Rahoton dake shigo mana yanzu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta labaran da ke yawo a kafafen yada labarai kan cewa hukumar yaki da rashawa, EFCC, ta kama shi.

Tsohon gwamnan ya tabbatar da cewa, da kan shi ya kai wa hukumar ziyara har ofishinsu domin wanke sunansa kan wani korafi da aka kai gaban ta a kan shi.

An ruwaito Kwankwaso ya ziyarci hedkwatar hukumar domin ya sanar da abinda ya sani kan zargin, inda ya kara da cewa da kan shi ya je hukumar kuma ya gana da wasu jami’an hukumar na wasu sa’o’i.

Kwankwaso ya kwatanta korafin da zugar ‘yan siyasa tare da zargin cewa ‘yan siyasan da ke son ganin sun tozarta shi ne suka kai korafin.

A matsayi na na dan kasa nagari mai kiyaye doka, da kai na na ziyarci hukumar a ranar Lahadi domin wanke kai na kuma babu shakka hakan ne ya faru”. “Na hadu da jami’an EFCC kuma na ce zan wanke sunana ne kan korafin da aka rubuta a kai na tun shekaru shida da suka gabata.

Labarai Makamanta