Kwamitin majalisar wakilan Najeriya kan sauya fasali da musanya tsoffin kuɗi ya yi fatali da ƙarin wa’adin kwana 10 da Babban Bankin ƙasar ya yi na amfani da tsoffin takardun kuɗi.
A wata sanarwa da gwamnan Babban Bankin Godwin Emefiele ya fitar ranar Lahadi ya ce shugaban ƙasar Muhammdu Buhari ne ya sahale wa CBN ɗin yin ƙarin wa’adin zuwa ranar 10 ga watan fabrairu.
To sai dai a martanin kwamitin ƙarƙashin jagorancin shugaban masu rinjaye na majalisar Alhassan Ado Doguwa, ya yi watsi da ƙarain wa’adin, yana mai cewa dole CBN ya yi biyayya da sashe na 20, ƙaramin kashi na 3, da 4 da kuma 5 na dokar CBN.
Idan za a iya tunawa dai a ranar Talata ne majalisar ta kafa kwamitin da zai duba batun wa’adin da CBN ɗin ya saka, bayan ‘yan ƙasar da dama sun yi ta kokawa kan irin wahalhalun da suke sha a ƙoƙarinsu na musanya kuɗadensu.
Doguwa ya ce “Wa’adin kwana 10 da CBN din ya ƙara ba mafita ba ne, mu abin da kawai muke buƙata a matsayinmu na ‘yan majalisa shi ne CBN ya yi biyayya ga sashe na 20 ƙaramin kashi na 3 da na 4 da kuma na 5 na dokar CBN”.
” A matsayin Najeriya na ƙasa mai tasowa, kuma mai bin tafarkin dimokradiyya dole mu yi biyayya da abinda doka ta tanadar.
Ya ƙara da cewa majalisar wakilan za ta bayar da umarnin kamo gwamnan Babban Bankin domin tilasta masa bayyana a gaban kwamitin.
Doguwa ya ci gaba da cewa kwamitinsa zai ci gaba da aiki har sai ya tabbatar da biyan buƙatun ‘yan ƙasar kamar yadda doka ta tanadar.
Yayin da yake bayyana ƙarin wa’adin kwana 10 da cewa ba wani abu ba ne illa yaudarar ‘yan ƙasar tare da ƙara jefa tattalin arzikin ƙasar cikin halin ni-‘yasu, Doguwa ya ce dole ne gwamnan Babban Bankin ya bayyana a gaban Majalisar wakilan ko kuma ya fuskancoi barazanar kama shi, ta hanyar yin amfani da ƙarfin da doka ta bai wa majalisar.
Doguwa ya kuma ce matakin na Babban Banki na iya yin barazana ga babban zaɓen da ke tafe.
You must log in to post a comment.