Karbar Dala: Kotu Ta Amince Ganduje Ya Sauya Lauya

Babbar kotun jihar Kano ta amince a zaman ta na jiya Litini cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sauya shaidu da lauyoyin da ke kare shi a shari’ar da ake yi a tsakaninsa da dan jarida Jafar Jafar, mai wallafa jaridar Daily Nigerian ta intanet.

Tun a ranar 10.11.2020 Gwamna Ganduje ya nemi hakan amma lauyan Jafar Jafar ya nuna rashin amincewarsa. Sai dai a zaman kotu na Litinin din nan alkali Suleiman Baba Namalam ya ce Gwamna Ganduje na da ‘yancin da zai iya sauya shaidu da lauyoyin nasa. An kuma dage sauraran shari’ar sai ranar 20.04.2021 don ci gaba da ita, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ganduje da Jafar Jafar dai sun shiga kotu ne bayan da dan jaridar ya wallafa wasu bidiyo wanda a cikinsu ake zargin Gwamna Ganduje da cusa Dalolin kudade a aljihunsa da ake zargin cin hanci ne daga ‘yan kwangilar da gwamnatinsa ke ba kwangilar ayyuka a jihar Kano, zargin da Gwamna Ganduje ya yi saurin musantawa.

Labarai Makamanta