Karba-Karba Matsalace A Siyasar Najeriya – Sheikh Jingir

Daga Adamu Shehu Bauchi

Shahararren Malamin Addinin Musulunci na Izalatul-bidi’a wa-ikamatus-sunnah Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir, yace Shugabancin kasa na Karba-Karba matsala ce ga Siyasar Najeriya, a cewarsa babu yancin da ake magana kowa na dashi ta wajen zaben Shuwagabbanni na siyasa a matakai dabam-dabam.

Malamin yayi wan nan bayani ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a wajen taron wa’azi na kasa da kuma addo’oi na musamman ga Najeriya, wanda ke gudana a filin wasa na Abaubakar Tafawa Balewa dake Jihar Bauchi.

Sani Yahaya Jingir yace, lokaci yayi da kowani dan Najeriya zai tashi tsaye ta wajen zaben Shuwagabanni na gari, Wanda mutane suke ganin ya chan’chanta ba wai don alakarsa daga wani bangare yake ba,

kana yace, duk inda mutum ya fito sai aduba chan-chantarsa ba alakan shi da cewa ga daga inda ya fito ba, domin yin hakan ba siyasa have, abar mutum ya zabi abunda yake so.

Kana Malamin ya sake Jan hankalin Musulmai da su yankin katin zabe a duk inda suke, saboda shine hanyar da zasu bi don su zabi mutum mai nagarta kuma jajirtace.

San nan Malamin yace maganar tsaro akwai sa hannun wadanda basu son Najeriya ta ci gaba da zama a matsayin kasa dunkulalliya, musamman daga kasashen ketare,

Shima Shugaban Kungiyar reshen jihar Bauchi Sheikh Salihu Sulaiman Ningi, yace taro irin wan nan yana dada Kara dankon zumunci tare da dinke maraka a tsakanin Musulmai da cingaba, da hadin kai, kana yace dama Abunda Alkur’ani mai Tsarki yake fadi shine ku riki juna ki samu hadin Kai ban da rarrabuwa, domin bashi alfanu.

Sulaiman Ningi, ya karkare da cewa taron ya samu halartan manyan baki daga sassan afrika ta yamma da kuma jama’ar musulmai daga sassan Najeriya baki daya.

Labarai Makamanta