Karar PDP: Matawalle Zai San Matsayinsa A Shekarar Badi

Biyo bayan karar da jam’iyyar adawa ta PDP ta kai Gwamna Bello Matawalle, A ranar Talata, 2 ga watan Nuwamba, 2021, babbar kotun tarayya da ke garin Abuja ta saurari karar da jam’iyyar PDP ta shigar kan Gwamnan na Jihar Zamfara da ‘yan Majalisar Jihar.

Jam’iyyar hamayya ta PDP tana karar gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle a kan sauya-sheka da ya yi, zuwa jam’iyyar APC mai mulki, bayan ya yi nasarar lashe zabe a jam’iyyar PDP.

PDP tana so a sauke duka sauran ‘yan majalisun Zamfara da suka sauya-sheka tare da Gwamnan sannan a mayar da mukamansu ga ‘ya’yan jam’iyyar PDP.

PDP ta shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/650/2021 ta hannun lauyanta, James Onoja tun a watan Satumba. Amma sai bayan wata daya aka sa lokacin da za a zauna.

Alkali Inyang Ekwo ya sa 18 ga watan Junairun 2022 a matsayin ranar da za a saurari karar da aka shigar, da kuma yanke hukunci akai.

Labarai Makamanta

Leave a Reply