Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gamayyar Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam a Najeriya sun yi kira cikin gaggawa ga Buhari da Gwamnan Babban Banki Godwin Emefiele su yi murabus daga mukamansu sakamakon gazawa wajen magance matsalar kudi.
A wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban gamayyar kungiyoyin Emmanuel Onwubiko yace kungiyoyin sun koka kan irin halin ko in kula da gwamnan babban banki Emefiele, da shugaba Buhari suka yi wa umurnin kotun kolin, inda ya ce sun gallaza wa ‘yan Najeriya azaba kan rashin kudi bayan da suka sauya fasalin Naira 200, 500 da 1,000.
Ya ce Buhari da Emefiele sune suke tafiyar da kasar yadda suke so ba tare da tausayin halin da ‘yan kasa suke ciki ba. Yace kungiyar bata yarda da irin wannan mataki da zai sake ruguza tattalin arzikin kasar ba, saboda haka yana kira ga Emefiele da Buhari da su yi murabus.
You must log in to post a comment.