Karancin Fetur Na Addabar Birnin Tarayya Abuja

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar masu ababen hawa a birnin na ci gaba da fuskantar dogayen layuka a gidajen mai sakamakon karancin man fetur da birnin ke fuskanta tun makon da ya gabata.

A wata sanarwa da hukumar da ke kula da sufuri da rarrabawa da tace mai ta kasar (NMDPRA) ta fitar ta ce ambaliyar ruwa da ake fuskanta a jihar Kogi ne musabbabin karancin man da birnin ke fuskanta.

Ambaliyar dai ta tilasta wa gomman motocin dakon man makalewa a kan hanya sakamakon mamaye babban titin da ya hada kudanci da arewacin kasar.

Mafiya yawan gidajen man birnin na ci gaba da kasancewa a rufe, kuma kalilan din da ke a bude dogayen layuka sun yi musu yawa, yayin da ‘yan bumburutu ke cin karensu babu babbaka a birnin.

Labarai Makamanta