Kanu Da Igboho Ke Rura Wutar Kyamatar Fulani A Kudanci – Gumi

Mashahurin Malamin addinin Musuluncin nan mazaunin Garin Kaduna Sheikh Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi, ya zargi shugabannin ‘yan aware biyu; Nnamdi Kanu da Sunday Igboho da laifin tada rikici a kudancin Najeriya, dake jefa rayuwar Fulani cikin hatsari.

Kanu, shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) da Igboho da ke kira ga kafa kasar Yarbawa dukkansu suna tsare a hannun gwamnati, bisa zargin haddasa fitina a Najeriya.

Sheikh Gumi a lokuta da dama ya na kare ‘yan bindigar da ke kashe mutane, yana mai cewa bai kamata a ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda ba, maimakon haka kamata ya yi ayi musu afuwa sannan gwamnati ta dauki nauyin su.

A cewar Gumi, sace-sacen mutane da kashe-kashen da ake dangantawa da wasu Fulani makiyaya a Kudancin Najeriya bai isa ya sa ‘yan awaren su nemi ballewa daga kasar ba. Gumi ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa ta yanar gizo mai taken; “Musulunci da rawar da malaman addini suka taka wajen samar da zaman lafiya a rikicin ‘yan bindiga a Arewa maso yammacin Najeriya”.

Malamin ya ce: “Kuma wani abin da na lura a Kudu shi ne, akwai bambanci tsakanin matakin ilimi da sanin ya kamata. Kuma idan akwai irin wannan rashin daidaito, rikici ba zai taba karewa ba saboda da wuya mutane su fahimci juna.

Labarai Makamanta