Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Kwamishinan Shari’a na jihar yace gwamna Abdullahi Umar Ganduje yace zai sa hannu kan hukuncin rataya da kotu ta yankewa Mallam Abduljabbar ba tare da ɓata wani lokaci ba.
“Matsayar gwamna bai sauya ba kan sanya hannu akan hukunci da kotu ta yanke” 5 “Akwai matakan da ya kamata a bi kuma a shirye mai girma gwamna yake da zarar an kawo masa zai sanya hannu”
“Babu wanda za a bari ya taka doka, kuma an dauki duk matakin da ya kamata a dauka” “Mun gurfanar da Abduljabbar a gaban kotu ne domin bashi duk dama ta kare kansa, kuma Alhamdulillah kotu ta gamsu da hujjojin da muka gabatar shi yasa ta yanke masa hukunci”
A cewarsa hukuncin kotun ya wanke gwamnatin jihar Kano da ke nuna ba wani shafaffe da mai, sannan gwamnatin zata tabbatar da hakan bai sake faruwa ba.
You must log in to post a comment.