Gwamnan jihar kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne a gurin bikin fara gabatar da rigakafin cutar maleriya da aka yi a fadar masarautar Bichi a jiya.
Gwamnan ya ce kudin hadin gwaiwa ne tsakanin Gwamnatin Kano da kungiyar yaki da cutar maleriya ta duniya.
Ganduje yace wannan shirin ya zama dole sakamakon yadda cutar maleriya take kashe yara da mata a jihar Kano. Inda ya ce za a gudanar da rigakafin a daukacin kananan hukomomin jihar Kano 44.
Bikin kaddamar da rigakafin ya samu halartar mataimakin Gwamnan Kano Dakta Nasir Yusif Gawuna, Mai Martaba Sarkin Bichi Alh Nasiru Ado Bayero, kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa da sauran manyan mukarabban Gwamnati.
You must log in to post a comment.