Kano: Za A Rataye Mawakin Da Ya Yi Batanci Ga Annabi

Wata kotu da ke jihar Kano ta Najeriya ta yanke wa wani mawaki hukuncin kisa bayan ta same shi da laifin batanci ga Annabi Muhammad [SAW]

Babbar Kotun ta Shari’ar Musulunci da ke Hausawa Filin Hockey, ta yanke wa Yahya Sharif mai shekaru 22 hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Bayanai na cewa, Sharif ya yi batancin ne a cikin wata waka da aka yi ta yada ta a shafukan WhatsApp a cikin watan Maris na wannan shekara, lamarin da ya sa masu zanga-zanga suka kona gidan iyalan mawakin, sannan suka yi tattaki har zuwa Shalkwatan Hukumar Hisbah mai kula da lamurran addini a jihar ta Kano.

Mahaifin mawakin, Aminu Sharif, wanda tuni ya yi hannun riga da dan nasa, yace ba’a a gidansa yake ba a lokacin da ya aikata laifin batanci ga addinin Musulunci.

Sharif ya kuma kara da cewa akidansa da na dan nasa sun sha bambam.

Labarai Makamanta