Kano: ‘Yan Daba Sun Hallaka Ɗan Sanda

Wasu ‘yan Daba da ba a san ko su wanene ba sun hallaka wani jami’in dan sanda a birnin Kano.

Lamarin ya faru ne a jiya a unguwar kureken-Sani dake yanki karamar hukumar Kombotso a jihar Kano.

Wata ‘yar uwar mamacin ta shedawa majiyarmu cewa maharan dauke da makamai sun shiga har gidan jam’in dan sandan, inda suka yi masa kisan gilla a gaban matarsa da ‘dansa

Dan sandan da aka hallaka yana cikin tawagar jami’an tsaron da suke tsaron Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero.

Labarai Makamanta