Kano: Tsige Shugaban Majalisar Malamai Ya Bar Baya Da Kura

Wani ɓangare na manyan malaman Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya sun yi watsi da batun sauke Sheikh Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malaman jihar da wasu malaman suka yi iƙirarin yi a ranar Litinin.

Hakan ya zama tamkar samun rabuwar kai a tsakanin shugabancin Majalisar Malaman

Malaman da suka yi iƙirarin sauke Malam Ibrahim Khaleel sun zargi shugabancinsa ne da shiga siyasa tare da rashin faɗaɗa Majalisar Malaman zuwa ƙananan hukumomi.

Sai dai wasu masu riƙe da manyan muƙaman shugabancin Majalisar na cewa waɗanda suka sauke malamin ba ƴan Majalisar Malaman ba ne.

Ɓangaren da ke iƙirarin sauke Sheikh Khalil dai ya ce sun maye gurbinsa ne da shugaban ƙungiyar Izala na jihar Sheikh Saleh Pakistan.

Sai dai gwamnatin Jihar Kano ta ce babu hannunta a lamarin.

Wannan lamari dai ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin al’umma a jihar da kuma sauran masu bayyana ra’ayoyinsu a shafukan sada zumunta, inda kowa ke fassara lamarin da irin fahimtarsa.

Me ya faru tun farko?

A wani taron manema labarai ranar Litinin a Kano, sakataren gamayyar ƙungiyoyin Izala da Ƙadiriya da Tijjaniya, Malam Jamilu Abubakar, ya ce sun sauke Malam Ibrahim Khalil ne saboda shiga harkokin siyasa.

“Bayan maganar da ta shafi siyasa akwai kuma wasu da suke manya-manya ne a Majalisar da ba za su iya fito na fito da jagoorancin ba”.

To ko ɓangaren da ke ja da sauke Malam Khalil ya taɓa tuntuɓarsa kan waɗannan ƙorafe-ƙorafen?

Sai Malam Jamilu ya ce ‘an yi hakan a baya, akwai manya-manyan malamai da suka je suka tuntuɓe shi.”

Wasu na ganin ba Malam Khalil ne kawai malamin da ya taɓa shiga harkar siyasa ba amma sai a wannan karon aka ɗauki mataki, sai dai Malam Jamilu ya ƙara da cewa “mu ba mu da alaƙa da Gwamnatin jihar Kano don haka sauke shin ba shi da alaƙa da mu’amalarsa da gwamnati, damuwarmu ita ce a gyara Majalisar a samar da majalisa mai karsashi.”

Sai dai wasu daga cikin malaman da suka halarci taron na Litinin sun ce ba su da masaniyar me za a yi a wajen taron kuma sun buƙaci a ba su damar magana amma aka ce an zartar da hukunci a madadinsu.

Malam Sulaiman Ƙiru ɗaya ne daga cikin malaman da ke da irin wannan koke, inda ya ce: “Ai ba taro aka kira mu za a sauke shugaba ba, kiranmu taro aka yi aka ce an zauna an sauke shugaba.

“A wajen taron ma na yi tambaya. Ba kiranmu aka yi muka sauke wani muka zaɓi wani ba.”

Malam Sulaiman ya kuma yi kira ga malamai da su ji tsoron Allah a duk abin da za su yi. “Ya kamata Malamai su sun cewa su magada Annabi Muhammadu (SAW) ne. Komai dabara komai wayo abin da babu goyon bayan Allah a cikinsa ba zai tabbata ba.”

Haka zalika ɗaya daga cikin malaman wanda ya buƙaci BBC ta sakaya sunansa ya ce reshen ƙungiyar na ƙaramar hukumarsu ne ya kawo su wajen taron, sai dai ya ce abin da aka yi a wajen ba shi da maraba da siyasa.

“Wannan ƙaramar hukumarmu ce ta kira mu wannan taro bisa ga buƙatar kansu. Mu kuma muka amsa kira, sai da muka zo aka yi mana bayani aka ce ana so mu ba da goyon baya.

“Amma gaskiyar magana yaya za ka bayar da goyon baya a kan abin da ba ka da hujja a kansa? Mu dai wannan abu ya haska mana lamari ɗaya, an ce kar a yi siyasa amma kuma an zo an yi siyasar,” a cewarsa.

Wannan layi ne

‘Wasu malaman sun ce ba ruwansu’

Dr Sa’id Ahmad Dukawa shi ne kakakin Majalisar Malamai ta Kano, ya ce har yanzu Malam Ibrahim Khalil ne shugaban Majalisar Malamai a Kano, domin kuwa waɗanda suka bayar da wannan sanarwa ba ƴaƴan ƙungiyar ba ne.

Wata sanarwa da aka fitar mai ɗauke da sa hannun Dr Dukawa a ranar Talata, ta ce malamai 10 da aka sanya sunayensu a sanarwar ba su san da maganar ba.

Malaman su ne:

  • Farfesa Muhammad Musa Borodo
  • Sheikh Ƙaribullah Nasiru Kabara
  • Sheikh Abdulwahab Abdallah
  • Sheikh Ibrahim Shehu Maihula
  • Farfesa Muhammad Babangida Muhammad
  • Dr Bashir Aliyu Umar
  • Imam Nasir Muhammad Adam
  • Dr Ibrahim Mu’azzam Mai Bushira
  • Dr Sa’idu Ahmad Dukawa.

Sanarwar ta ce “Jagororin zauren haɗin kan malamai da ƙungiyoyin Musulunci na jihar Kano sun samu labarin wata sanarwa da wasu mutane suka bayar suna iƙirarin sauke Sheikh Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta jihar Kano, tare da ayyana wanda suke sha’awar ya shugabance ta.

“Jagororin suna tabbatar wa al’umma cewa ba da yawunsu aka yi wannan jawabi ba kuma ba sa goyon bayansa.

“Har kullum jagororin suna neman zaman lafiya ne da haɗin kan al’umma, amma wannan yunƙurin zai haifar da saɓanin hakan ne.

“Don haka zaure yana kira ga al’umma da su ci gaba da ririta zaman lafiyar Kano su guji duk wani abu da zai iya zama barazana ga tsaro da kwanciyar hankali,” kamar yadda sanarwar ta ce.

sanarwa

Sanarwar ta ce “Jagororin zauren hadin kan Malamai da kungiyoyin Musulunci na jihar Kano sun samu labarin wata sanarwa da wasu mutane suka bayar suna ikirarin sauke Sheikh Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta jihar Kano, tare da ayyana wanda suke sha’awar ya shugabance ta.

“Jagororin suna tabbatar wa al’umma cew aba da yawunsu aka yi wannan jawabi ba kuma ba sa goyon bayansa.

“A har kullum jagororin suna neman zaman lafiya ne da hadin kan al’umma, amma wannan yunƙurin zai haifar da saɓanin hakan ne.

“Don haka zaure yana kira ga al’umma da su ciu gaba da ririta zaman lafiyar Kano su guji duk wani abu da zai iya zama barazana ga tsaro da kwanciyar hankali,” kamar yadda sanarwar ta ce.

Wannan layi ne

Me gwamnatin Kano ta ce?

BBC ta tuntuɓi kwamishinan harkokin addinai na jihar Kano Dr Muhammad Tahar Adamu wanda ake kira da Baba Impossible wanda ya ce bai san komai kan maganar ba.

Sai dai da muka tuntuɓi Kwamishinan Ƴaɗa Labarai Muhammad Garba ya musanta zargin, yana cewa gwamnati ba ta da hannu a sauke Malam Khalil.Ya kuma musanta zargin da wasu malaman suka yi cewa shugabanninsu na ƙananan hukumomi ne suka ce su zo su halarci taron da aka yanke hukuncin sauke malamin.

“Babu wani malami da gwamnati ta nemo shi ya zo ya sauke Sheikh Ibrahim Khalil,” in ji Kwamishina Garba

Sai dai kwamishinan ya ce a yanzu su duk wanda ya fi rinjayen magoya baya daga cikin malaman biyu da ake ƙiƙi-ƙaƙa a kansu shi ne wanda gwamnatin jihar Kano za ta yi mu’amala da shi.

Wannan lamari na faruwa ne makonni kaɗan da Majalisar Malaman ta Kano ta yi zargin cewar akwai yunƙurin da wasu ke yi na neman sauke shugabansu Malam Ibrahim Khalil daga kan muƙaminsa, inda suka yi wani taro na nuna goyan baya tare da yin mubaya’a a gare shi.

Sai dai a wancan lokacin ba su iya fitowa sun ambaci waɗanda suke zargi da hannu a lamarin ba.

Labarai Makamanta