Kano: Shugaban Majalisar Malamai Ya Sauya Sheka Zuwa ADC

Shugaban Majalisar Malamai ta Ƙasa, Sheikh Ibrahim Khalil ya sauya sheƙa zuwa Jam’iyar ADC.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a ƙarshen 2021 ne Sheikh Khalil ya baiyana ficewar sa da ga Jam’iya mai mulki ta APC amma bai baiyana wacce ya koma ba.

Sai dai kuma a yau Juma’a ne Sheikh Khalil ɗin ya baiyana ADC a matsayin jam’iyyar da ya koma.

Bayanin komawa jam’iyyar ADC da malamin ya yi, na kunshe cikin wani sako da shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Shu’aibu Ungoggo, ya gabatar ga manema labarai.

Cikin bayanin na sa, Shu’aibu Ungoggo, ya ce malamin ya shigo jam’iyyar ta su ta ne tare da Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa na jami’ar Bayero, da kuma wasu malaman jami’a guda takwas da su ka rufa masa baya, a kokarinsu na ganin cewa an ceto jihar Kano daga halin da ta ke ciki.

Ya kuma baiyana cewa nan gaba kadan za’a shirya taron karbar Sheikh Khalil a jam’iyyar.

Labarai Makamanta