Kano: Sheikh AbdulJabbar Ya Soki Lamirin Lauyoyinsa

Labarin dake shigo mana daga Birnin Kano na bayyana cewar an sake kwatawa a babbar kotun shari’ar musulunci ta Kano, yayin da Sheikh Abduljabbar Kabara, ya sake neman a ba shi dama ya kare kansa, bisa zargin Lauyoyinsa sun gaza.

Rahotanni sun bayyana Shehin malamin ya sake sa’in sa da lauyoyin dake kokarin kareshi a shari’ar da ake masa kan zargin batanci. Dama tun farkon lokacin da gwamnatin Kano ta gurfanar da shi a gaban Kotu, Malamin ya ƙalubalanci lauyoyinsa da zarginsu, wanda ya tilasta musu aje aikin.

A ranar Alhamis, Malamin wanda ake zargi da batanci ga Manzon Allah (SAW), laifin da hukuncinsa kisa ne a addinin musulunci, yace shi bai yarda da lauyoyinsa ba. A cewarsa, lauyoyin ba su da cikakken ilimin addinin musulunci sosai, don haka a bashi dama ya kare kansa.

A zaman kotun na ranar Alhamis Lauyan ɓangaren masu shigar da ƙara, ya gabatar da shaidarsa ta biyu, wani mutumi mai suna Murtala Kabir Muhammad. Murtala mazaunin Kofar Na’isa Lokon Makera ya bayyana wa kotu cewa shi ɗalibin sheikh Abduljabbar ne.

Yayin da aka nemi ko ɓangaren da ake ƙara suna da tambayoyi ga shaidan, lauyan Albduljabbar ya bayyana wa kotu cewa wanda yake kare wa yana son a bashi dama ya kare kansa.

Barista Muhamamd Amin Kabir, ya kafa hujja da sashi na 36 (6d) na kundin mulkin Najeriya wanda aka yi wa garambawul.

A hukuncin da ya yanke kan haka, alƙalin kotun, Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, yace ɓangaren da ake ƙara suna da damar zaɓen wanda zai kare, ko wanda ake ƙara ya kare kansa ko kuma tawagar lauyoyinsa su kare shi.

Ɓangaren lauyoyin gwamnati sun bayyana cewa duk da Malamin ya nemi ya rinƙa kare kansa, amma ya zama wajibi sai yana da Lauyoyi a shari’ar. Bayan sauraron dukkan ƙorafe-korafen ɓangarorin biyu, Alkalin ya ɗage zaman har zuwa 11 ga watan Nuwamba 2021.

Labarai Makamanta