Kano: Satar Yara Na Nema Zama Ruwan Dare

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar matsalar satar yara na sake bulla a Birnin Kano, daya daga cikin birane mafiya girma a Najeriya.

Hakan ta kai ga wasu mata neman a ba su damar kafa kwamitin tsaron yara domin dakile wannan dabi’a. Ko a baya dai gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin da zai yi bincike kan bace-bacen yaran wadanda ake zargin ana safararsu ne zuwa wasu sassan kasar.

Sai dai iyaye da dama da yaran nasu suka bace na zargin kwamitin da jan kafa wurin gudanar da ayyukansa.

Labarai Makamanta