Kano: Sanusi Ya Kauce Haɗuwa Da Bayero

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya juya tare da ‘yan rakiyarsa daga shiga harabar Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, ana hasashen Sarkin ya ɗauki matakin hakan ne saboda halartar Sabbin Sarakuna daga Masarautun Bichi, Gaya da Rano, wajen bikin yaye dalibai na farko a Jami’ar.

Wannan mataki da Sarkin ya ɗauka ya jefa jama’a da yawa cikin mamaki a waje taron. Saboda an ji kade-kaden motarsa da bushe bushen kakaki, amma sai ya juya ya bar filin taron.

An samu ra’ayoyi mabanbanta akan matakin da Sarkin ya ɗauka, wasu su na cewa ya yi daidai, wasu kuma suna inkarin haka, saboda an sanar da zuwan Sarkin kafin juyawarsa.

Related posts