Labarin dake shigo mana daga birnin Kano na bayyana cewar Fitaccen mawakin siyasa nan na Hausa Dauda Kahutu Rarara, wanda ya yi fice wajen yi wa Shugaba Muhammadu Buhari waka, ya saki sabuwar waka inda ya soki Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano.
Mawaƙi Dauda Rarara, wanda shine shugaban kungiyar siyasa ta Kannywood, 13X13, ya kasance cikin masu yaba wa Ganduje kuma ya bada goyon baya a manyan zabukan 2015 da 2019.
An tattaro cewa mawakin baya goyon bayan Dr Nasiru Yusuf Gawuna, ɗan takarar gwamna na APC a Kano, maimakon haka, ya bayyana goyon baya ga Sha’aban Ibrahim Sharada na Action Democratic Party, ADP.
Amma ya jaddada cewa har yanzu shi ɗan APC ne kuma yana goyon bayan takarar shugaban kasa na Tinubu/Shettima a zaɓen shekarar 2023.
A cikin sabuwar wakar da ya fitar a ranar Laraba don yi wa Tinubu kamfen, Rarara ya tabbatar da rikicinsa da Ganduje kuma ya bayyana gwamnan a matsayin ‘Hankaka’, ma’ana mutum mai fuska biyu.
A cikin wakar, Rarara ya ce: “Ka ce su cire suna na kuma na ji, amma ban taba cewa a saka suna na ba. Na san dukkan tarurrukan da ka ke yi. Za mu bada gudunmawarmu ga Tinubu ba tare da muna wata tawaga ba. Kai hankaka ne kuma za mu nuna maka mune gwanayen waka….”.
You must log in to post a comment.