Kano: Sabon Rikici Ya Kunno Kai Tsakanin Ganduje Da Kwankwaso

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin yin sulhu tsakanin tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da magajinsa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wani sabon rikicin siyasa ya sake kunno kai tsakaninsu.

Yayin wata hira da jaridar Punch a ranar Asabar, Kwankwaso ya bayyana nasarar da Ganduje ya samu a zaɓen 2019 a matsayin haramtacciya, yana cewa wasu gaggan ƴan siyasa ne daga sama suka ƙaƙaba wa al’ummar jihar Kano shi.

“Sun tursasa wa ɗumbin mutane ra’ayin wasu ƴan tsiraru wanda hakan shi ne laifi mafi muni a tsarin dimokuradiyya. Ina tsammanin sun fahimci kuskurensu a yanzu, wasunsu na ƙoƙarin gyara kura-kuransu a yanzu bayan barnar da aka yi wa jihar Kano. Abin takaici ne yadda suka kasa ganin abin da talakawa suka hango wa kansu.”

Ya ci gaba da cewa ”Muna da ƙarfin da za mu iya hana su abun da suka so yi a wannan lokaci, amma muka buƙaci matasanmu su kwantar da hankalinsu, muka bar su da aniyarsu, muka bi matakin shari’a, amma a nan ma aka yi abun da aka yi” in ji Kwankwaso.

Sai dai wata sanarwa da ta fito daga fadar gwamnatin jihar Kano mai ɗauke da sa hannun Kwamishinan Watsa Labaran jihar Muhammadu Garba, ta bayyana kalaman na Kwankwaso a matsayin shaci-faɗi da ko kaɗan babu ƙanshin gaskiya a cikinsu.

”Abun takaici ne yadda a matsayin Kwankwaso na shugaba, wanda ake damawa da shi a harkokin gudanar da zaɓe ya kasa amincewa da sakamakon zaɓen da hukuma mai zaman kanta ta gudanar kuma kotu ta amince da shi”

Hirar da Kwankwason ya yi da jaridar Punch ta janyo masa mummunar illa ne fiye da alfanun da ya yi tsammanin za ta haifar masa.

Labarai Makamanta