Kano: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Tabbatar Da Sace Tsohon Shugaban Tashoshin Jiragen Ruwa

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da sace tsohon janar manajan hukumar tashoshin jiragen ruwa na Najeriya, Bashir Abdullahi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, DSP Haruna Abdullahi ya fitar, kuma aka rarraba ta ga manema labarai a birnin Kano ranar Alhamis.

“An tura wata tawagar tsaro ta Operation Puff Adder domin su ceto wanda abun ya rutsa da shi tare da kama masu laifin.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A ranar 03/11/2021 da misalin karfe 1630, mun samu wani rahoton cewa, wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace wani Bashir Abdullahi mai shekaru 65 na kauyen Sitti, karamar hukumar Samaila, jihar Kano, a gonarsa da ke dajin Barasa, kauyen Gomo, karamar hukumar Sumaila, jihar Kano, wanda ke kan iyaka da jihar Bauchi.

“Da samun rahoton, kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya tashi sannan ya umarci tawagar tsaro na Operation Puff Adder da su ceto mutumin sannan su kama masu laifin.”

Labarai Makamanta