Kano: PDP Ta Dakatar Da Kwankwaso Da ‘Yan Kwankwasiyya

Jam’iyyar PDP reshen jihar kano ta dakatar da tsohon gwamna jihar kuma jigo a siyasar kano da kasa baki daya, sanata Rabi’u Musa Kwankwanso da dukkan magoya bayan darikar kwankwasiyya daga shiga duk wata harkar Jam’iyyar ta PDP na tsawon watanni uku.

Sanarwan hakan ya fito ne daga sakataren Jam’iyyar PDP reshen jihar kano, H,A Tsanyawa ya sawa hannu jim kadan bayan zaman da masu ruwa da tsakin Jam’iyyar suka gudanar yau.

Ana Bukatar Kwankwaso yayi bayanan kare kansa daga zargi aikata manyan laifuka uku da aka gatar akan sa kamar haka:

Ana zargin sa da tarwatsa taron zaben shuwagabannin shiyyar arewa maso yamma da aka gudanar a kaduna ranar 10 ga wannan wata da muke ciki.

Ana kuma zargin sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da durawa gwamnoni biyu dake wurin taron ashar.

Sai kuma ana zargin magoya bayan darikar kwankwasiyya da lalata kayayakin da aka tanada don gudanar da wannan zabe a makon jiya a Kaduna.

Biyo bayan wannan korafe korafen da muka samu ne muka Yanke hukuncin cewa ‘ Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya zo ya wanke kanshi daga wa’innan zarge zargen da ake masa,kuma Jam’iyya ta dakatar dashi na wata uku kamar yadda tsarin kundin mulkin PDP ya tanada a sashi na 59 (1) (2) (3) (4).

Labarai Makamanta