Kano: Matashin Da Ya Zagi Ganduje A Facebook Ya Gamu Da Fushin Kotu

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar wata kotun majistiret dake zamanta a Kano, ta hana Matashin da ake zargi da yiwa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, batanci rubutu a dandalin Facebook.

Kotun ta ɗauki wannan matakin ne a zamanta na ranar Litinin, 8 ga watan Nuwamba, 2021 yayin zaman cigaba da sauraron ƙarar.

BBC Hausa ta buga a shafinta na Facebook cewa Alkalin kotun, Mai shari’a Aminu Gabari, ya kuma janye belin da ya baiwa wanda ake zargin, Muazu Magaji Danbala kiru.

Alkalin ya ɗauki matakin janye belin ne biyo bayan gaza cika sharuɗɗan da aka gindaya masa, kuma lauyansa ya nuna cewa sharuɗɗan sun yi tsauri.

Shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa dake cikin kwaryan birnin Kano, Auwalu Aramfo, shine ya kai karar mutunen biyu, Muazu Magaji Danbala da kuma Jamilu Shehu.

Honorabul Aramfo ya garzaya gaban hukumar tsaro ta farin kaya yana neman a kwatar wa gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, haƙƙinsa kan mutanen. A cewarsa waɗanda ake zargin sun bata wa gwamna suna da kuma wasu daga cikin iyalansa a shafin sada zumunta ta hanyar kiransu da barayi, masu karkatar da kuɗaɗen al’umma.

Bayan sauraron ƙarar a yau Litinin, Mai shari’a Aminu Gambari, ya ɗage sauraron shari’ar har zuwa ranar 29 ga watan Nuwamba, 2021.

Labarai Makamanta