Kano: Malaman Jami’ar Bayero Sun Koma Bakin Aiki

Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar malaman Jami’ar Bayero sun koma bakin aiki a ranar Litinin bayan kungiyar malaman jami’o’i ASUU ta sanar da janye yajin aikin da suka shafe wata takwas suna yi.

Dalibai da ma’aikata sun fara shiga jami’ar a ranar Litinin inda suka bayyana farin cikinsu tare da fatan za a fara daukar darasi.

Kungiyar dai ta ce ta rubuta wa hukumar jami’ar Bayero Kano cewa malaman sun dawo bakin aiki.

Yayin da malaman jami’ar suka janye wannan yajin aiki, ga alama, shirye-shirye sun kankama na ci gaba da daukar darasi a jami’ar Bayero Kano.

Labarai Makamanta