Kano: Makasan Hanifa Sun Samu Lauya

Rahotanni daga jihar Kano na bayyana cewa Antoni janar na jihar kuma kwamishinan shari’a, Barista Musa Abdullahi Lawan, ya bayyana cewa Majalisar taimako ta sharia’a ta ƙasa ta bayyana bukatar wakiltar Abdulmalik Tanko da sauran wadanda ake zarginsu da kisan yarinya mai shekaru biyar, Hanifa Abubakar.

Antoni janar din ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis cewa, wannan ya biyo bayan umarnin Mai shari’a Usman Na’abba na babbar kotun jihar Kano ne a ranar 5 ga watan Fabrairu inda ya ce jihar ta samarwa da Tanko da sauran mutum biyun lauya.

Lawan ya ce duk wanda ke fuskantar shari’a kan zargin kisan kai, ana bukatar ya samu lauya kuma idan mutum ba shi da lauya sannan ba shi da halin samowa, gwamnatin tarayya ta bukaci jiharsa da ta samar masa.

Ya yi bayanin cewa Majalisar shari’ar ta Najeriya kafuwar gwamnatin tarayya ce wanda aikinsu ya kama da samar da lauya kyauta ga duk dan Najeriyan da bashi da lauya kuma ake zarginsa da kisan kai wanda hukuncinsa kai tsaye na kisa ne.

“Tawagar lauyoyinmu a shirye suke da su gabatar da gamsassun shaidu kan Abdulmalik Tanko da sauran mutane biyun, amma ba zai yuwu a cigaba ba. Idan muka samu aka yanke hukunci a kansu ba tare da lauya ba, babu shakka za a soke shari’ar idan aka daukaka kara.”

Ana zargin Tanko da wasu mutum biyu da garkuwa tare da halaka Hanifa kuma shari’ar ta tsaya saboda rashin lauyan wadanda ake zargin. Bayan da alkali mai shari’a ya bayar da umarnin a samar musu da lauya, ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Fabrairu mai zuwa.

Labarai Makamanta