Kano: Labarin Kisan Hanifa Ya Tada Hankula


Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana Dangi da ƴan uwan yarinyar nan Hanifa da ake zargin malaminta ya sace tare da kashe ta, kana ya binne gawarta a gidansa a jihar Kano na ci gaba da alhinin rasuwarta.

Ranar Alhamis rundunar ƴan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta tabbatar gano gawar Hanifa Abubakar a wani kabari da aka binne ta bayan an kashe ta.

Cikin kuka da hawaye, mahaifin Hanifa, Malam Abubakar Abdussalam, ya shaida wa BBC Hausa cewa sun shiga cikin mummunan tashin hankali sakamakon lamarin da ya faru, har ta kai ga an kwantar da mahaifiyar marigayiyar a asibiti.

“Lokacin da mahaifiyar ta samu labari ta kaɗu, mun kai ta asibiti yanzu haka an sa mata ruwa an ba ta magunguna, ba ta iya ko cin abinci kullum sai kuka, ni kaina bana iya cin abinci ba na iya barci,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa “Ina ofishin Hukumar DSS aka kirawo ni aka sanar da ni cewa ga shi an gano gawarta, don haka suka ba ni haƙuri suka ce ƙaddara ce daga Ubangiji in yi haƙuri.”

Labarai Makamanta