Kano: Kotu Ta Tabbatar Wa Sagagi Da Shugabancin PDP

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano a ranar Talata ta yi watsi da umarnin da ta bayar a baya na hana shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Shehu Sagagi da ya riƙa nuna kan sa a matsayin shugaban jam’iyar a jihar.

Ana zargin dai Sagagi yana biyayya ga tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso.

A ranar 17 ga Mayu ne dai, Justice A.M. Liman ya bayar da umarnin dokar wucin gadi ta hana shugabannin PDP da Sagagi ke jagoranta a Kano yin duk wani iko har sai an saurari koke-koken kudirin nasa.

Wani Bello Bichi ne ya kai karar INEC da PDP da wasu mutum 40 gaban kotun.

Da yake ba da umarnin a ranar Talata, Mai shari’a Liman ya ce wanda ya shigar da kara, Bello Bichi, ya yaudari kotun da cewa akwai gaggawa a kan lamarin.

Ya ci gaba da cewa Bichi ba shi da hurumin shigar da ƙarar saboda bai nuna hujjar cewa shi mamba ne a kwamitin zartarwa na jam’iyyar ba.

Don haka mai shari’a Liman ya ɗage sauraren ƙarar zuwa ranar 26 ga watan Mayu domin sauraren ƙarar.

Labarai Makamanta