Kano: Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Wa Abduljabbar Hukunci

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Kotun Shari’ar Musulunci da ke birnin ta saka ranar 15 ga watan Disamban 2022 don yanke hukunci kan tuhume-tuhumen da ake yi wa malamin nan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

Gwamnatin Kano na tuhumar shehin malamin da yin ɓatanci ga Annabin Musulunci Muhammadu S.A.W. kuma an tsare shi tun daga watan Yulin 2021.

Abduljabbar zai sake bayyana a gaban Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola na kotun da ke Ƙofar Kudu ne bayan ƙungiyar lauyoyi masu bai wa marasa gata kariya ta ce bai cancanci su ba shi kariyar ba saboda yana samun fiye da naira N30,000 duk wata.

An nemi a ba shi kariyar ce sakamakon lauya Ambali Muhammad ya fice daga kariyar da yake bai wa Abduljabbar a shari’ar a watan Yuni da ya gabata.

Kafin tsare shi, Abduljabbar ya yi iƙirarin cewa kare Annabin yake yi maimakon ɓatanci kamar yadda ake zargin sa, abin da ya sa gwamnatin Kano ta shirya muƙabala tsakaninsa da wasu malamai a jihar.

Alƙalin muƙabalar ya yanke hukuncin cewa Abduljabbar bai amsa tambayoyi da ƙalubalen da aka yi masa ba game da kalaman da yake yi kan Manzon Allah a lokacin muhawarar kamar sauran takwarorinsa.

Sai dai malamin, wanda ɗa ne ga shahararren jagoran ɗariƙar Ƙadiriyya Malam Nasiru Kabara, ya yi zargin rashin adalci daga masu shirya muƙabalar kuma ya nemi a sake shirya wata daban, abin da gwamnatin ta yi watsi da shi.

An gudanar da muƙabalar bayan malamin ya gabatar da karauka daban-daban yana mai neman a zauna muhawarar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply