Kano: Kotu Ta Daure Matashin Da Ya Kira Ganduje Barawo A Facebook

Rahotanni daga birnin Kano na bayyana cewar wata kotu da ke zamanta a Nomansland ta bada umurnin a tsare wani Matashi mai suna Mu’azu Magaji Danbala saboda taɓa mutuncin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Ana tuhumar wanda ake zargin ne da furta kalaman cin mutunci ga gwamnan da yaransa biyu; Abdulaziz da Balaraba a shafin sada zumunta na Facebook.

Ɗayan wanda ake zargin mai suna Jamilu Shehu har yanzu bai shigo hannu ba. An gurfanar da mutanen biyu ne kan hadin baki, zagi da gangan, tada zaune tsaye da ɓata suna wanda hakan sun saba da sashi na 97, 114, 391 da 399 na Penal Code.

A cewar bayanin farko, a ranar 26 ga watan Oktoban 2021, shugaban ƙaramar Hukumar Nasarawa, Auwal Lawal Shuaibu ya shigar da korafi wurin hukumar binciken sirri na musamman, SIB, kan mutanen biyun mazauna Ƙiru a Kano.

Rahoton na farko ya ce: “A ranar da aka ambata da farko, ku biyu kun haɗa baki kun wallafa hotunan mai girma Gwamnan Kano, har da yaransa biyu ɗauke da rubutu mai cewa ‘Ɓarayin Kano’ tare da sanin cewa abin da kuka aikata zai iya tada rikici a Kano da wajen Kano. “Don haka ana zargin ku da aikata laifukan da aka ambata tunda farko.”

Sai dai waɗanda ake zargin sun musanta aikata laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa kuma suka nemi beli. Daga nan kotu ta bada umurnin a tsare mata wanda ake zargin bayan ƙin amincewa da bukatarsa ta neman beli.

An dage cigaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Nuwamban 2021.

Labarai Makamanta