Rahotannin dake shigo mana yanzu daga Jihar Kano na bayyana cewar Wata Babbar kotun Shari’ar Musulunci ta Kofar Kudu a birnin Kano ta sake hana bayar da belin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.
Lawyan Abduljabbar Nasiru kabara, Muhammad A Mika’il ne ya gabatar da bukatar gaban mai Shar’ia Ibrahim Sarki Yola gabanin kammala zaman kotun a yau.
Gwamnantin jihar Kano ce dai ta ke karar Abduljabbar Nasiru Kabara bisa zargin batanci ga Manzon Allah da kalaman da ke tunzura jama’a.
You must log in to post a comment.