Kano: Jigon PRP Ya Kwanta Dama

Ɗaya daga cikin mutanen da suka ragewa ƴan mazan jiya da suka yi gwagwarmaya domin ƴantar da talaka daga ƙangin bauta, cin zali, musgunawa da noman gandu, biyan haraji da jangali Alhaji Muhammadu Dauda Ɗangalan ya amsa ƙiran mahalicci a jiya Asabar.

Tuni aka yi jana’izar sa da misalin ƙarfe biyar na yammacin jiya a gidansa dake unguwar Fagge a birnin Kano.

Marigayin ya bayyana a wata shira da jaridar Daily trust cewar ya fara siyasa yana ɗan shekaru 21 a duniya kuma dalilin shigarsa siyasa shine saboda ana zalintar talaka, ana saka shi yin aiki mai wahala da noman gandu, an mayar dashi bawa ana cutar dashi da hefa shi a cikin matsi.

An taɓa ɗaure shi yayi watanni shida a gidan yarin Kurmawa a lokacin gidan yarin an yi shine domin horo da saka mutane a cikin damuwa, yace da aka tashi faɗa masa laifinsa kawai ance yana ƙoƙarin tunzura talakawa su yiwa masu sarauta bore.

Yace manyan abokan siyasarsa sune Musan Musawa, Shehu Shatatima, Sani Darma, Adamu Danjaji, Malam Aminu Kano, Salihi Iliyasu, Garba Muhammad Gumel, Tanko Yakasai, Magaji Ɗanbatta, Babba Ɗan Agundi.

Shine mutumin da ya zagaya Gusau, Tsafe, Ƙauran Namoda, Maradun da sauran garuruwa domin nemowa NEPU magoya baya kuma ya bayyana cewar lallai zagayen da yayi ya samu darussa da sanin garuruwa da al’umma kuma an samu nasarar da ta kamata.

Ya ce shi sana’ar ɗinki ya haɗa da siyasa kuma ta rufa masa asiri sosai ta taimaka masa wajen yin harkokinsa yadda ya kamata.

Marigayi Aminu Kano shine mutumin da ya fi bashi gudunmawa tare da koyon abubuwa na haƙuri, juriya, tsayawa akan manufa, gaskiya da jure azaba ko baƙar wahala domin a ƙarshe a cimma burin da aka saka a gaba. Yace shi kam Alhamdu lillah a wajensa ƙwalliya ta biya kuɗin sabulu domin a kowanne mataki na muƙami a ƙasar nan yanzu ƴaƴan talakawa ne suka kai.

A wani taro da aka taɓa gudanarwa na ƴan mazan jiya da taron Talakawa Summit a Jigawa yace shi kam babu abinda zai ce da Alhaji Sule Lamido sai godiya da fatan alheri bayan ya sake fitowa da manufa da aƙidun NEPU/PRP kuma yayi aiyyukan da kowa yake alfahari dasu, yace yana taka muhimmiyar rawa wajen tallafa min ni da iyali na.

Allah ya jiƙan Dattijo Alhaji Dauda Ɗangalan ya gafarta masa kurakurensa, ya albarkaci bayansa.

Labarai Makamanta