Kano: Jaruma Sadiya Haruna Ta Fita Daga Daurin Talala

Fitacciyar matashiyar nan da ke amfani da kafofin sada zumunta, Sadiya Haruna, ta kammala ɗaurin-talalar da wata kotun shari’a da ke Jihar Kano a arewacin Najeriya ta yi mata.

Mai magana da yawun hukumar kula da gidajen yarin jihar, DSP Musbahu Lawan Kofar Nasarawa ne ya tabbatar wa BBC Hausa labarin a ranar Talata.

Alkalin kotun Mai shari’a Ali Jibrin ya yanke wa Sadiya Haruna hukuncin ɗaurin-talala na wata shida, inda ya yi umarni ta riƙa zuwa makarantar Islamiyya domin koyon “tarbiyya” da kuma “sanin yadda za ta riƙa mu’amala a matsayinta na Musulma”.

Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Jibrin ya umarci jami’an hukumar Hisbah su riƙa raka ta makaranta sannan su kai masa rajista domin ya tabbatar tana zuwa.

An yi wa matashiyar daurin-talala ne bayan da a watan Agustan da ya wuce rundunar Hisbah ta kama ta bisa zargin “yaɗa hotunan batsa” a shafukanta na sada zumunta.

Sai dai a wani sakon murya da ya turo wa BBC, DSP Musbahu, ya ce “a yau wannan baiwar Allah mai suna Sadiya Haruna ta kammala wa’adin ɗaurin-talalar da aka yi mata domin koyon tarbiyya na tsawon watanni shida”.

A cewarsa: “Tun lokacin da muka karbe ta mun sanya ta a makaranta domin ta rika koyon tarbiyya, kuma Alhamdulillahi, daga cikin abubuwan da ta koya sun hada da tarbiyar kanta da litattafai da suka hada da Alkur’ani da Hadisai da makamantansu.”

Ya kara da cewa matashiyar ta koyi darussa da dama game da rayuwa a tsawon wa’adin da ta kwashe tana cikin ɗaurin-talala.

Sadiya Haruna ta shahara a shafukan sada zumunta, inda take wallafa bidiyo da hotuna na harkokin ƙashin kanta ko kuma tare da wasu fitattun matasa, musamman a Youtube da Instagram.

Kamun da hukumar Hisbah ta yi mata ya jawo zazzafar muhawara, lamarin da ya sa wata tauraruwa a Kannywood, Ummah Shehu, ta yi zargin cewa “jami’an hukumar suna aikata laifuka amma sun ki duba nasu suna takura wa talakawa marasa galihu”.

Dag bisani, Hisbah ta nemi tauraruwar ta je gabanta domin ta yi mata karin bayani kan zargin da ta yi wa wasu jami’anta.

Labarai Makamanta