Kano: Jagorar Masu Zanga-Zanga Ta Mika Wuya

Ɗaya da ga cikin jagororin zanga-zangar #NoMoreBloodshed in Kano state, Zainab Naseer Ahmed ta nisanta kan ta daga zanga-zangar, jim kaɗan bayan ta dawo daga ofishin ƴan sandan farin kaya, DSS.

DSS ɗin ne dai su ka gaiyace Zainab domin tambayoyi sakamakon sa hannun ta a zanga-zangar da a ka haɗa a wasu jihohin arewa domin jawo hankalin gwamnati a kisan gillar da a ka yi wasa wasu matafiya 42 a Sokoto.

Bayan ta shafe wajen awanni biyu a hannun DSS ɗin, sai gani a kai Zainab ta wallafa a shafin ta na facebook cewa ta zare hannun ta daga zanga-zangar.

“Ina son mutane ku sani cewa daga yau na zare hannuna daga zanga-zangar da a ka fara yau, ina son kowa ma yayi haka.

“Na san akwai wasu abubuwa kuma na damu da zaman lafiyar alumma kuma bana son wani ya samu rauni ko jikkata.

“Gaskiya haɗari ne yin zanga-zanga yanzu a Kano saboda rahoton da na samu ya nuna cewa wasu ɓatagari na nan ma shirin amfani da zanga-zangar domin kawo tarzoma,”

“Ina mai baku shawarar da ku yi zaman ku a gida domin “zaman lafiya ya fi zama ɗan sarki”,

Labarai Makamanta