Kano: Hisbah Ta Kori Jami’inta Da Aka Kama Da Matar Aure A Hotel

Rahotanni daga birnin Kano na bayyana cewar Hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta sallami Sani Nasidi Uba Rimo, daya daga cikin kwamandojinta da akayi zargin an kama da matar aure a Otal.

Kakakin hukumar, Lawal Fagge, ya tabbatar da hakan ranar Talata ga manema labarai.

Ya ce kwamitin da ta gudanar da bincike kan zargin da akayi masa ta kamasa da laifi.

Rimo, ya kasance babban jami’in da yake yaki da karuwai a jihar Kano. Amma an samu mishkila lokacin da aka yi zargin an kamashi da wata matar aure a Sabon Gari, a watan Febrairu.

Lokacin da aka tambayesa menene alakarsa da matar, an ruwaito cewa ya ce yar uwarsa ne, kuma ya ajiyeta a Otal ne don ta samu matsala da mijinta.

Sakamakon haka kwamanda Janar na Hisbah, Ustaz Harun Muhammad Ibn Sina, ya nada kwamiti don binciken lamarin.

Labarai Makamanta