Kano: Hisbah Ta Kama Matashin Da Ya Yi Yunkurin Sayar Da Kanshi

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Rundunar Hisbah a jihar ta kama wani matashi mai shekaru 26 da ya sa kan sa a kasuwa domin sayarwa saboda talauci.

A wata tattaunawar sa da manema labarai a Kano kwamanda janar na rundunar, Sheikh Harun Ibn-Sina ya bayyana hakan. Ibn-Sina ya ce sun kama matashin ne saboda abinda ya aikata ya ci karo da koyarwar addinin musulunci.

Ibn Sina ya ce babu wani dalili a musulunce da zai sa mutum ya sanya kan sa kasuwa domin sayarwa.

A tattaunawar, kwamanda janar din Hisbah ya nuna rashin dacewar mutum ya aikata hakan inda ya ce musulunci bai yarda da wannan dabi’ar ba.

“Eh, mun kama shi jiya da daddare kuma a wurin mu ya kwana sai dai ba mu zauna da shi mun tattauna ba tukunna. “Da safen nan zan same shi don in ji ta bakin sa.”

Matashi Aliyu wanda tela ne ya tattauna da manema labarai kafin a kama shi. Ya shaida mu su cewa fatara ce dalilin da ya sa ya ke neman siyar da kan sa a N20,000,000.

Labarai Makamanta