Kano: Hadimin Ganduje Ya Yi Ɓatan Dabo

Da sanyin safiyar yau Asabar mutane sun fara boren #FreeDawisu a shafin sadarwar zamani ta Twitter, wata majiya ta shaida mana cewar wannan bore ya biyo bayan batan dabo da Salihu Tanko Yakasai ya yi.

Majiyoyi sun bayyana cewar Salihu ya bace ne jiya bayan wasu rubuce rubucen da ya yi akan satar mutane dake cigaba da durkusar da yankin arewacin ƙasarnan.

Wasu bayanai na bayyana cewar hukumar DSS ne ta yi awon gaba da shi, sakamakon rubuce-rubucen nashi da ake gani suna da nasaba da harkar tsaro.

Sai dai har yanzu bamu samu wani sahihin labari daga makusanta Salihu ba, yayinda dukkanin wayoyin wadanda suke da kusanci dashi suka kasance a kashe

Labarai Makamanta