Kano: Ganduje Ya Kaddamar Da Babura Na Musamman Ga KAROTA

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya kaddamar da babura na musamman guda 25 ga hukumar rage cinskoso ta jihar, KAROTA, domin dakile cinkoso a jihar, da tabbatar da bin doka da oda.

Da ya ke kaddamar da baburan a ranar Lahadi a Kano, Ganduje yace za a yi amfani da baburan ne domin tabbatar da cewa masu ababen hawa suna bi doka da oda a fadin Jihar mafiyawan jama’a a Arewa.

Ya ce baburan za su ba jami’an KAROTA damar ratsa wurare cikin gaggawa domin sanya ido kan yadda masu saba dokokin tuki da gano masu shigo da haramtattun ababe zuwa jihar.

Gwamnan ya bukaci jami’an na KAROTA su zage damtse a kokarinsu na kula da cinkoson ababen hawa da kama masu saba doka. Ya kuma bukaci su tabbatar an rika kama wadanda ke shigowa da haramtattun ababe zuwa jihar.Ganduje ya yabawa shugaban KAROTA, Baffa Dan’agundi saboda bullo da wannan sabon tsarin.

Tunda farko, Dan’agundi ya ce an siyo baburan ne da kudaden da aka samu bayan korar ma’aikatan bogi a hukumar.

“Wasu lokutan, muna ganin abubuwa da dama suna faruwa, muna ganin miyagu suna daukan haramtattun abubuwa cikin motoci amma babu motocin da za mu bi su zuwa wurin da za su tafi mu kama su. “Amma, da wannan sabbin baburan, za mu iya kama masu laifi da dama,”.

Labarai Makamanta