Kano: Ganduje Ya Biya Jaafar Jaafar Diyar ₦800,000

Mai girma Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abdullahi Umar Ganduje, ya biya diyyar kudin har ₦800,000 da kotu ta bukata ga sanannen ɗan Jaridar nan Jafar Jafar, wanda ya fallasa Bidiyon Dala kamar yadda Alkali ya umarce shi.

Shugaban gidan jaridar na Daily Nigerian, Jaafar Jaafar ya nuna cewa wadannan kudi sun shigo hannunsa a wani bayani da ya yi a shafinsa na Facebook.

‘Dan jaridar ya kyankyasa wannan ne a safiyar Juma’a, 19 ga watan Nuwamba, 2021.

Bayan haka, ‘dan jaridar ya shaidawa gidan rediyon Freedom na garin Kano cewa an biya shi kudin kamar yadda Alkali ya bada umarni a watan Yuli.

Labarai Makamanta