An bayyana Farfesa Sagir Adamu Aliyu a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar zama shugaban jami’ar Bayero dake Kano bayan fafatawa da aka yi tsakanin ‘yan takara.
Farfesa Sagir Adamu ya yi nasarar zama shugaban jami’ar bayan ya samu kuri’u 1026 yayin da Farfesa Tanko Adamu ya zo na biyu da kuri’u 416. Sai Farfesa M.D Mustapha da ya zo na uku da kuri’u 10 kacal.
Da wanan sakamakon ne Farfesa Sagir Adamu ya dare kujerar shugaban jami’ar ta Bayero (Vice Chancellor) bayan Farfesa Muhammad Yahuza Bello wa’adinsa ya cika.
You must log in to post a comment.