Kano: Dr. Junaidu Mohammed Ya Rasu

Rahotanni daga birnin Kano a tarayyar Najeriya na bayyana cewar Ɗan Majalisar wakilai a Jamhuriya ta biyu mai wakiltar Kano, Dakta Junaid Mohammed ya riga mu gidan gaskiya cikin daren jiya.

Daya daga cikin ‘ya’yan Marigayin mai suna Suleiman Mohammed ya tabbatar da rasuwar, inda ya ce ya rasu a daren ranar Alhamis yana da shekaru 73 a duniya bayan fama da rashin lafiya na kwanaki uku.

Iyalansa za su sanar da lokacin gudanar da jana’izarsa nan gaba kaɗan. Tawagar manyan mutane a ciki da wajen birnin na kano sun fara tururuwa zuwa gidan Marigayin da ke No. 60 Lamido Crescent a Kano don yi wa iyalinsa ta’ziyya.

Marigayi Junaidu Mohammed yana daya daga cikin ‘yan siyasan da aka kafa jam’iyyar People’s Redemption Party (PRP) tare da su a shekarar 1976 karkashin shugabancin marigayi malam Aminu Kano.

Ya kuma rike mukamin mataimakin shugaban Social Democratic Party (SDP) na kasa a yankin Arewa maso Yamma. Allah muke roko ya jiƙansa ya gafarta mishi Allahumma amin.

Labarai Makamanta