Kano: Dalilin Rikicina Da Murtala Sulen Garo – Ado Doguwa

Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhaji Alhassan Ado Doguwa, ya yi bayanin abin da ya haddasa sabani tsakaninsa da Murtala Sule Garo.

Rahotanni sun bayyana cewar Honorabul Alhassan Ado Doguwa ya isa gidan Nasiru Gawuna ɗan takarar kujerar Gwamnan Kano ƙarƙashin Jamiyyyar APC inda ake zaman APC, ya koka kan yadda aka ware shi a gefe.

‘Dan majalisar wakilan kasar ya fadawa jagororin APC ba a neman shi a kan abubuwan da suka shafi kudi, sai dai idan za ayi wa jam’iyya wani aiki. Wannan ya jawo rikici ya shiga tsakaninsa da Murtala Garo mai takarar mataimakin gwamna.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata, Honorabul Ado Doguwa yace bai je wajen taron jam’iyyar domin fada da Garo ba, ya je ganin shugaban jam’iyya ne.

“Ban je da nufin halatar taron ba, na je ganin Abdullahi Abbas ne, in yi tafiya ta. Da na isa gidan Gawuna, na shiga dakin taron, sai na iske ana zama. Sai nayi ba’a ga mataimakin gwamna, nace ya kamata a samu wakilci daga majalisa.

Sai Murtala ya tsoma baki, ‘dole ne a gayyace ka?’, dole ne a gayyaci ‘yan majalisar tarayya. Sai ya fara dirka mani zagi “banza maras mutunci, dan uban ka ba za a gayyace ka ba”.

“Ban maida masa martani ba saboda ina da tarbiyya. Sai ya cigaba da zagi na, har ya nemi ya ja mani riga, daga nan nayi fushi, na fara martani. Ta kai ya nemi ya ci kwala ta, a yunkurin zuwa ya yi fada da ni, akwai kofi a kan tebur, Sai Murtala Sule Garo ya bugi kofin da ya fadi, ya tarwatse.

Labarai Makamanta