Kano: Dakatarwar Da Aka Yi Mini Jarrabawa Ce – Sheikh Khalil

Daga karshe Sheikh Ibrahim Khalil ya yi jawabi bayan barkewar rikici wanda ya kai ga dakatar da shi daga matsayin shugaban majalisar malamai na jihar Kano.

Sheikh Khalil ya bayyana rikicin a matsayin nufin Allah, wanda ya ce ya gwada shi domin ya ga karfin imaninsa a matsayinsa na Musulmi,

Malamin ya yi magana ne a Kano a ranar Asabar, 23 ga watan Oktoba, lokacin da ya karbi bakuncin Majalisar Tabbatar da Shari’a a Najeriya.

Majalisar ta bayyana dakatar da babban malamin ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin a jihar Kano. An kuma maye gurbinsa da Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, a matsayin shugaban rikon kwarya.

Sai dai kuma, dakatarwar ta hadu da turjuya daga malamai daban-daban a jihar. Amma da yake magana a ranar Asabar, Sheikh Khalil ya ce: “Allah ya yi alkawari gwada mu a komai. Abun da ya faru shakka babu abu ne da Allah ke so ya yi amfani da shi don ganin karfin imaninmu a tafarkinsa.

“Ina kallon hakan a matsayin gwaji, amma nagode Allah ya nuna mana duk daya muke, amma duk haka muna neman yafiyar Allah. “Ina kuma godiya ga dukkan wadanda suka tsaya tsayin daka don ganin an samu hadin kai, ciki harda wadanda ma ba malamai bane.

“Irin haka abu ne da muke alfahari da shi. Zan ci gaba da nuna godiya ga dukkan wadanda suka nuna damuwa da kuma wannan majalisa ta Shariah.”

Da yake jawabi a madadin Majalisar Shari’ar, Malam Jamilu Mu’azu Haidar, ya ce sun zo Kano ne a madadin kungiyar ta kasa, don nuna goyon bayansu ga shugabancin Khalil.

Haidar wanda ya kasance mamba a Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya ce sun saurari bayanai daban-daban kan rikicin sannan an ba su tabbacin cewa babu hannun gwamnatin jihar a ciki.

“Muna kira ga sauran malamai da su ji tsoron Allah su dawo a ci gaba da tafiya tare, kamar yadda Sheikh Khalil yake kokarin yi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply