Kano: Cutar Amai Da Gudawa Ta Hallaka Mutum 15

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar a kalla mutum 15 ne suka rasa rayukansu a kauyen Koya dake karamar hukumar Minjibir ta jihar Kano bayan zargin barkewar cutar amai da gudawa a yankin.

Dagacin kauyen, Malam Sulaiman Muhammad, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai inda yace annobar ta fi shafar mata da kananan yara.

Mazauna kauyen da suka zanta da manema labarai sun ce wadanda cutar ta shafa suna ta kwarara amai da gudawa babu ƙaukautawa.

Jami’an lafiya da suka isa kauyen bayan aukuwar lamarin sun hori mazauna kauyen da su guji shan ruwa daga tafkuna da rijiyoyin kauyen.

An tattaro cewa jami’ai sun kai jakkuna ruwan leda 300 kauyen a ranakun karshen mako domin takaita cigaban yaduwar muguwar annobar.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Aminu Tsanyawa, bai dauki wayar da aka dinga kiransa ba domin jin martanin gwamnatin jihar a kan lamarin.

Labarai Makamanta